Hukumomin Australia sun kame mutane 17 da yunkurin kai harin taáddanci | Labarai | DW | 08.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Australia sun kame mutane 17 da yunkurin kai harin taáddanci

Yan sanda a kasar Australia sun ce sun gano wata makarkashiya ta kaiwa kasar gagarumin harin taáddanci kuma tuni ta kame mutane goma sha bakwai wadanda ake tuhuma da wannan yunkuri. Rundunar yan sandan ta baiyana cewa an kame mutane takwas a birnin Sydney ragowar mutanen tara kuma a Melbourne. Zaá gabatar da mutanen goma sha bakwai a kotu a yau Talata. Rundunar yan sandan bata baiyana wuraren da aka yi niyar kaiwa harin ba, sai dai ta ce wadanda ake zargi sun kai mataki na karshe na aikata harin taáddancin. An sami wasu sinadaran magunguna a tare da su wadanda aka ce suna shirin yin amfani da shi wajen sarrafa makamashi na bom. Gwamnatin ta ce an kama mutanen ne bayan zartar da wasu dokoki tsaurara wadanda suka saukaka bin didigin masu laifi. Yan adawa sun soki lamirin dokar da cewa ta na tada hankali alúma.