Hukumomin Algeria sun yi belin Ali Belhadj daga kurkuku | Labarai | DW | 07.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomin Algeria sun yi belin Ali Belhadj daga kurkuku

A saban yunkurin su na tabbatar da zaman lahia, da kuma yafe wa juna, hukumoim,Algeria sun yi, belin pirsinoni fiye da dubu 2, a makon da ya gabata.

Wannan Pirsinoni sun haɗa da mataimakin shugaban russasar jami´iyar FIS, Ali Belhadj ,da a ka yi beli a yammacin jiya.

A watan julin da ya gabata ne, a ka sake capke Ali Belhadj, bayan, ya yabawa yan ta´adar kasar Iraki, da ke ci gaba da kai hare hare.

Ya yi wannan kalamomi, jim kaɗan bayan hallaka wasu jami´an diplomatia 2, na Algeria a birnin Bagadaza.

Ranar 21 ga watan febriaru da ya wuce, shugaban ƙasar Alegria Abdukl Aziz Buteflika, ya sa hannu akan dokar afuwa, ga pirsinonin, kamar yadda saban kudin tsartin mulkin ƙasar ya tanada.

Mafiyawan pirsinonin an kama su, a rikicin siyasa, da ya ɓarke a ƙasar, tun 1992, wanda kuma ,ya hadasa mutuwar mutane dubu 150.

A sakamakon wannan rikici, hukumomin Algeria,sun rusa jam´iyar FIS, mai tsatsauran ra´ayin addini Islama, su ka kuma capke, shugabanin ta wato Abassi Madani, da Ali Belhaj.

A wani labari kuma na daban,jiya ne shugaban majalisar dokokin ƙungiyar gamayya turai, Josef Borel, ya fara ziyara aikin kwanaki 3, a ƙasar Algeria.