Hukumomi a Iraki sun ba da sanarwar sakin firsinoni kimanin 500 daga Abu Ghraib | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumomi a Iraki sun ba da sanarwar sakin firsinoni kimanin 500 daga Abu Ghraib

Hukumomin Iraqi da na Amirka sun ba da sanarwar sakin firsinoni kimanin 500 daga kurkun Abu Ghraib dake yammacin birnin Bagadaza don bikin karamar Salla. Wata sanarwa da soji suka bayar ta ce saboda salla karama, ranar bikin kawo karshen azumin watan ramadana, gwamnatin Iraqi ta bukaci hukumar gidajen kurkuku dake aiki da dakarun kasashen waje a Iraqi da ta saki firsinoni 500 da ake tsare da su a kurkukun Abu Ghraib. Kakakin ma´aikatar kare hakkin bil Adama a Iraqi, Hisham al-Suhaili ya ce za´a sako firsinoni 565 daga Abu Ghraib don bikin karamar Salla, kuma za´a sako su gabanin a yi sallar idi a gobe laraba ko kuma jibi alhamis. Wannan afuwa dai ta shafi wadanda laifin su bai taka kara ya karba, inji kakakin.