1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar zabe ta pakistan a gobe zata yanke shwara kan ranar zabe

December 31, 2007
https://p.dw.com/p/CiZn

Hukumar zaɓe ta ƙasar Pakistan ta ce a ranar Talata zata sanarda shawara da ta yanke kan ko a gudanar da zaɓe a ranar 8 ga watan Janairu ko a a. Manyan jami’an gwamnati kodayake sun ce mai yiwuwa ne a dakatar da zaɓen da yan makonni. A dai ranar Lahadi ne jamiyar PPP ta zaɓi dan marigayiya Benazir Bhutto a matsayin wanda zai gaje ta. Bilawar Bhutto Zardari ɗan shekaru 19 da haihuwa ɗalibi ne a jamiar Oxford ta ƙasar Birtaniya, an naɗa shi shugaban jamiyar yayinda mahaifinsa Asif Ali Zardari zai riƙa kula da harkokin yau da kullum na jam’iyar. Mutane fiye da 40 ne dai suka rasa rayukansu cikin tarzoma da ta biyo bayan kashe Benazir a ranar Alhamis a birnin Rawalpindi.