1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar zabe a Liberia ta fara binciken karan magudi

Hukumar zabe mai zaman kanta, a kasar Liberia ta fara bincike a kan karan da dan takara Jorje Woyah ya shigar, na zargin magudi a zaben shugaban kasa zagaye na 2, zaben da Ellen Sirlif Johson ta lashe, tare da kussan kashi 60 bisa 100 na kuri´un da a ka jefa.

Hukumar zaben na da wa´adin kwanaki 30 kamin ta bayana saakmako wanna bincike saidai shugabar ta bayyana cewa za su gaggauta ta yada za su bayyana sakamakon kamin karshen wannan wa´adi.

A nasa gefe, tsofan shugaban kasar Nigeria, Jannar mai ritaya Abdusalami Abubakar, ya yi kira ga Jorje da ya amince da sakamakon binciken komin dacin sa.