Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana lokacin gudanad da zaɓe a ƙasar a shekarar baɗi. | Labarai | DW | 25.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar zaɓen Najeriya ta bayyana lokacin gudanad da zaɓe a ƙasar a shekarar baɗi.

Hukumar zaɓe ta taryyar Najeriya, ta gabatar wa maneman labarai lokacin da za a gudanad da zaɓen shugaban ƙasa da gwamnonin jihohi 36 na tarayyar, a shekara mai zuwa. Shugaban Hukumar, Maurice Iwu, ya bayyana cewa za a gudanad da zaɓen ne tsakanin ran 7 ga watan Ifrilu zuwa ra 28 ga wannan watan, a shekarar ta baɗi. Kawo yanzu dai, inji shi, hukumar ta kammala kusan kashi 70 cikin ɗari na ayyukan shirya zaɓen.

Jam’iyyun siyasa 37 ne rahotanni suka ce sun yi rajista da hukumar, waɗanda za su shiga takarar zaɓen sabon shugaban ƙasa, da zai gaji cif Olusegun Obasanjo, shugaba mai ci a yanzu. Zaɓen dai, shi ne zai kasance na 3, a ƙasar tun da aka kawo ƙarshen mulkin soji a shekara ta 1999.