Hukumar Zaɓe a Togo, ta gano kura-kurai a mazaɓun Lome | Labarai | DW | 21.10.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Zaɓe a Togo, ta gano kura-kurai a mazaɓun Lome

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a ƙasar Togo, ta jinkirta bayyana sakamakon yan majalisun dokoki a wasu mazaɓu da ke birnin Lome, a dalilin da kuraren da ta ce an tabka.

Tun ranar laraba da ta wuce hum,ura zabe ta bayana sakamakon wannan zaɓe, banda na birnin Lome.

Hukumar na jiran wannan sakamakon, wanda zai bada damar ƙayyade jam´iya, kokuma jam´iyun da za su samu kujeru 5 da ya rage a majalisar dokoki.

Sakamakon bayan fage da aka samu,ya nunar da cewa jam´iyar adawa ta UFC ke sahun gaba, a mazaɓun Lome baki ɗaya.

Wannan shine karon farko da jam´iyar adawa ta Gil Christ Olympio, ta shiga zaɓe a kasar Togo, ta kuma yi korafin cewar an tabka kura-kurai masu yawa, ta hanyar yin aringizon ƙuri´u, ga jam´iyar RPT mai riƙe da ragamar mulki.