1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta gaza wajen mutunta ka'idojin hukumar WADA

Kamaluddeen SaniMay 13, 2016

Hukumar yaki da shan kwayoyin sanya kuzari ta duniya wato WADA tayi kakkausan suka ga kasar Kenya a bisa rashin mutunta ka'idojin hukumar sau da kafa.

https://p.dw.com/p/1InBw
Symbolbild Doping
Hoto: picture-alliance/ dpa/dpaweb

Shugaban kwamitin sake bibiyar ka'idojin hukumar ya ce hukumar kasar Kenya kan gwaje gwajen sanya kwayoyi masu sanya kuzari basa mutunta dukkanin ka'idojin da aka shimfida kan gwaje -gwajen kamar yadda ya kamata.

Bugu da kari a hannu daya, kasar Rasha itama na daga cikin kasashen da ke fuskantar bincike akan badakalar afa kwayoyi ga 'yan wasan ta wanda hakan ka iya jefa su cikin jerin kasashen da hukumar zata iya haramtawa shiga wasanin motsa jiki na Olympic na Duniya da ake shirin yi a Kasar Brazil.

Kwamitin shirya wasanin na Olympic din dai shine kadai yake da gabarar bayyana dukkanin kasashen da zasu shiga wasanin da za a fara a watan Augustan shekarar nan a kasar Brazil muddin ya gamsu bayan tantance kasashen ba tare da samun su da laifin afa kwayoyi ba.