Hukumar UEFA ta zani sabon shugaba | Labarai | DW | 14.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar UEFA ta zani sabon shugaba

Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Turai UEFA ta zabi Aleksander Ceferin shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Sloveniya a matsayin sabon shugabanta wanda zai maye gurbin Michel Platini

Hukumar Kula da Wasannin Kwallon Kafa ta Turai UEFA ta zabi Aleksander Ceferin shugaban hukumar kwallon kafa na kasar Sloveniya a matsayin sabon shugabanta wanda zai maye gurbin Michel Platini tsohon shugaban kungiyar da aka tsige biyo bayan samun shi da aka yi da hannu a badakalar cin hancin da aka bankado a hukumar shirya wasannin kwallon kafa ta duniya wato FIFA.

Sabon shugaban hukumar ta UEFA dan shekaru 48 ya yi nasarar darewa kujerar ne bayan da ya samu kuri'u 42 daga cikin 55 zaben da aka gudanar inda ya kayar da abokin hamayarsa Michel Van Praag dan kasar Hollande mai shekaru 68 wanda ya samu kuri'u 13 kawai. Jim kadan bayan zaben nasa Aleksander Ceferin ya yi alkawarin baiwa marada kunya kan wannan nauyi da aka dora masa:

"Ya ce ina godiyya da wannan babban goyon baya da kuka bani, wanda kuma babbar daukaka ce amma kuma babban kalubale. dan haka ni da iyalaina da 'yan karamar kasata ta sloveniya na farin cikin da wannan, kuma ina fatan wata rana za ku yi farin ciki da ni"

Shi dai Aleksander Ceferin sabon shugaban hukumar ta UEFA wanda asalinsa lauya ne, ba sananne ba ne a fagyen wasannin kwallon kafa kamar Michel Platini da ya canza. Kuma babban kalubalen da ke a gabansa shi ne na tsarkake tsarin gudanarwa na hukumar a daidai lokacin da sunan duniyar wasannin kwallon kafa ya gurbace sabili da matsalar cin hanci da rashawa.