Hukumar turai tayi barazana ga wasu kasashe membobi | Labarai | DW | 12.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar turai tayi barazana ga wasu kasashe membobi

EU/CLIMATE

Hukumar turai tayi barazanar daukan matakan sharia akan wasu kasasahen turai 15 muddin dai basu bada bayanai gane da shirye shiryensu na rage garbatar yanayi a kasashensu.

An bukaci dukkanin kasahen kungiyar taraiyar turai 25 da su gabatar shirye shiryen su na rage guba da hayakin masaantu dake haddasa gurbacewar muhalli,kafin babban taron kula da muhalli na kungiyar da aka shirya a 2008.

Hukumar tace ta aike da takardun gargadi ga kasashe 15 da suka hada da Faransa Jamus,Hungary da Italy,bayan sun kasa cimma waadin watan yuni da aka baiwa kasashe membobi da su mika bayanan nasu.

Komishinan kula da muhalli na kungiyar Stavros Dimas yace yana da muhimmanci a mika wadannan bayani domin ci gaba da yaki da gurbatar yanayi karkashin yarjejeniya Kyoto ta 1997,inda kasashen turai suka amince rage hayakin masaanatu da kashi 8 bisa dari nan zuwa 2012