1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar turai tayi alkawarin taimakawa jama'ar Peru

Hukumar taraiyar turai tace zata bada akalla euro miliyan daya a matsayin agajin gaggawa ga wadanda girgizar kasa ta Peru ta rutsa da su.Wata sanarwa daga sasahen kula da jin kann jamaa na hukumar tace hukumar tayi alkawarin bada wannan kudi ne ne domin taikawa kungiyoyi masu zaman kansu da hukumomin MDD a yankunan da girgisar kasar ta shafa.Wannan taimako dai zai hada da samarda matsuguni da magunguna da kuma abinci.Har yanzu dai ana samun matsaloli wajen kaiwa ga wasu yankuna da abin ya shafa.Girgizar kasar da karfinta ya kai kashi 8 a maaunin Richter a kudancin Peru tayi sanadiyar akalla rayukan mutane 500 fiye da dubu daya kuma suka samu raunuka yayinda wasu dubbunnai kuma suka rasa gidajensu.