1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

hukumar turai ta kara sunaen jirage data haramtawa shiga turai

Hukumar taraiyar turai tace ta shirya sake duba jerin sunayen kanfunan jiragen sama da ta haramtawa jiragensu shiga nahiyar turai su hada da dukkanin kanfanonin jiragen sama 51 na kasar Indonesia,da wasu kanfanonin da dama na Rasha da Ukraine da Angola.

Jiragen saman kanfanin Garuda na Indonesia suke yawan zirga ziraga zuwa nahiyar turai.

Jamian KTT sunce an baiyana sunayen wadannan kanfanoni ne domin yin kashedi ga matafiya daga turai sun janye daga bin wadannan jirage tare kuma da ingiza kanfanonin kara inganta tsaro da lafiyar jiragen nasu.

Kwararru akan harkokin zirga zirgan jiragen sama na KTT suka saka sunayen kanfanonin na Indonesia ya biyo bayan haduran wasu jirage 4 na kasar Indonesia.

Hakazalika an haramtawa jiragen kanfanin Volare na Ukraine da kuma TAAG na Angola.