Hukumar leken asirin Jamus ta musanta ba dakarun Amirka taimako
January 13, 2006Tsohuwar gwamnatin SPD da kuma The Greens ta yi kanekane a rikicin Iraqi fiye da yadda aka sani kawo yanzu. Ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier da kuma hukumar leken asirin Jamus ta BND sun tabbatar da cewa an tura ma´aikatan hukumar zuwa birnin Bagadaza a lokacin yakin Iraqi. To amma sun musanta rahotannin cewar jami´an sun taimakawa sojojin Amirka a Iraqi. Da farko dai kafofin yada labarun Jamus da dama sun rawaito cewar a cikin shekara ta 2003, jami´an hukumar ta BND sun taka rawa a wani hari da sojojin kawance suka kai kan wani gidan cin abinci dake Bagadaza, inda aka halaka akalla fararen hula 12. Yanzu haka dai jam´iyun adawa sun yi kira da a gudanar da bincike akan rawar da hukumar ta taka a yakin Iraqi da kuma yakin da Amirka ke yi da ta´addanci na kasa da kasa.