Hukumar leken asirin Amirka ta faɗa halin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 08.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar leken asirin Amirka ta faɗa halin tsaka mai wuya

`Yan majalisar dattijan Amirka na ci gaba da kiran gudanar da bincike, game da hotunan bidiyon da akace hukumar leken asirin ƙasar ta lalata. Hotunan bidiyon dai na dauke da bayanai na gallazawa ne ga mutanen da ake zargi da aikata ayyukan ta´addanci. Lalata hotunan daga ɓangaren hukumar ta CIA a cewar ´Yan majalisar, abune da ya yi karan tsaye ga dokokin ƙasar. Tuni dai shugaban hukumar ta CIA, Michael Hayden ya ce an lalata hotunan bidiyon ne a shekara ta 2005, bisa kawo ƙarewar amfaninsu. A hannu ɗaya kuma da barazana da hotunan ka iya yi a gaba ga waɗanda ake zargi da aikata ayyukan na ta´addanci. Mr Hayden ya kuma ƙaryata zargin cewa an musgunawa waɗanda ake zargin a cikin hotunan. A cewar shugaban an ɗauki hotunan ne a shekara ta 2002, don amfanin cikin gida ga hukumar, a ƙoƙarin da take na yaƙi da ayyukan ta´addanci. Hukumomin kare hakkin bil adama dai sun zargi hukumar ta CIA da lalata hotunan bidiyon, don kaucewa zargin take hakkokin waɗanda take tuhuma.