1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar leken asiri ta Israila tace ta bankado yunkurin kashe shugaban Palasdinawa

May 7, 2006
https://p.dw.com/p/BuzJ

Hukumar leken asiri ta Israila tace ta kawadda wani yunkuri da yan kungiyar Hamas sukayi na kashe shugaba Mahmud Abbas.

Wata jaridar Burtaniya ta buga a yau cewa,bangaren Ezzadine Brigade na kungiyar Hamas ta shirya kashe shugaba Abbas a cikin ofishinsa dake gaza.

Jaridar tace hukumar leken asirin ta Israila ta sanar da shugaba Abbas wannan manakisa,inda ya soke ziyara da yayi niyar kaiwa zuwa yankin.

Majiyoyin leken asiri na Israilan sun baiyanawa jaridar cewa,kungiyar Hamas din ta shirya kashe Abbas da kuma wani minista na Palasdinun Mohammad Dahlan,dan jamiyar Fatah.

Majiyar tace jamian leken asiri na Israila suna sa ido akan dukkan take taken Hamas,saboda haka ne suka gano wannan manakisa,inda suka sanarda shi ba tare da bata lokaci ba.

Masu lura da alamura suna ganin cewa,Hamas ta dauki shugaba abbas a matsayin wani wanda ke hana mata ruwa gudu na gudanar da mulkinta a yankin Palasdinawa.