Hukumar leken asiri ta Amurka ta ce tuni Iran ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya | Labarai | DW | 03.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar leken asiri ta Amurka ta ce tuni Iran ta dakatar da shirinta na kera makaman nukiliya

Wani rahoton da hukumar leken asirin Amurka ta fitar ya baiyana cewa tun 2003 ƙasar Iran ta dakatar da shirinta na ƙera makaman nukiliya,haka kuma akwai alamun ta rage burinta na ƙera makama, ba kamar yadda tun farko gwamnatin Bush ta ɗauka ba.Rahoton ya ce ya zuwa tsakiyar wannan shekarar Iran bata koma shirinta na ƙera makaman nukiliyan ba duk da cewa taci gaba da inganta sinadaren uraniyum don a cewarta anfaninta a cikin gida.

Jami`an na Amurka sunce hakan ya nuna cewa bin hanyoyim diplomasiya yayi tasiri ga dakatar da shirin Iran na ƙera makaman.