1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar lafiya ta duniya ta yabawa kasar Turkiyya

January 11, 2006
https://p.dw.com/p/BvCl

Faraministan kasar Turkiyya, Tayyip Erdogan yace kasar sa ta samu shawo kann matsalar cutar murar tsuntsayen nan da a yan kwanakin nan tayi sular mutuwar wasu mutane a kasar.

Ya zuwa yanzu a cewar Erdowan, gwamnatin kasar ta bayar da umarnin kisan wasu tsuntsaye a kalla dubu dari uku da ake zargin na dauke da kwayar cutar ta murar tsuntsayen.

kasar ta turkiyya a cewar Erdogan, naci gaba da daukar matakan da suka dace don dakile yaduwar cutar murar tsuntsaye,a fadin kasar baki daya.

A waje daya kuma hukumar lafiya ta duniya, wato WHO cewa tayi , ta gamsu da irin matakan da kasar ta Turkiyya take dauka na dakile yaduwar wannan cuta, to sai dai ta kara da cewa shawo kann ta baki daya ka iya daukar watanni.