An gargadi kasashen daeke makotaka da Kwango
June 1, 2018Talla
Hukumar ta WHO ta shawarci kasashen da ke makwabtaka da kasar ta Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango da su dauki matakan gaggawa sakamakon yadda ake samun shige da ficen al'umma kusan dubu daya a kowace rana ta hanyoyin ruwa da jiragen sama.
Mutane 680 ne a halin yanzu suka samu rigakafin cutar a yankunan Mbandaka da Bikoro da aka fi samun yawaitar bullar cutar ta Ebola a kasar.