Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta ce an sami ƙarin mutane 5 da suka rasa rayukansu a ƙasar Indonesiya, sakamakon kamuwarsu da murar tsuntsaye. | Labarai | DW | 17.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta ce an sami ƙarin mutane 5 da suka rasa rayukansu a ƙasar Indonesiya, sakamakon kamuwarsu da murar tsuntsaye.

Hukumar Lafiya Ta Duniya, ta tabbatad da cewa, an sami ƙarin mutane 5 da suka rasa rayukansu a ƙasar Indonesiya, sakamakon kamuwarsu da ƙwayoyin cutar nan H5N1 na murar tsuntsaye, abin ya da kawo yawan waɗanda cutar ta halaka, zuwa 30 a ƙasar. Rahotannin da suka iso mana daga birnin Jakarta, sun ce, ban da Vietnam, yanzu Indonesiya ce ƙasa a jeri na biyu a duniya, inda aka fi samun yawan mace-macen mutane, sakamakon kamuwarsu da cutar.

Ana dai zargin gwamnatin Indonesiyan ne da rashin ɗaukan isassun matakai, kamar kashe dabbobin, wajen hana yaɗuwar ƙwayoyin cutar, waɗanda a halin yanzu suka shafi jihohi 27 daga 33 na kasar.