Hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD zata ta da sansanoninta dada gabashin Chadi | Labarai | DW | 21.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD zata ta da sansanoninta dada gabashin Chadi

Babban kwamishinan hukumar kula da ´yan gudun hijira ta MDD Antonio Guteres ya ce hukumar sa na duba yiwuwar mayar da sansanonin sa daga gabashin Chadi mai fama da rikici zuwa wuri mai tsaro dake tsakyiar kasar. A jiya da daddare shugaban na hukumar ya isa birnin N´jadmena don tattaunawa da FM Pascal Yoadimnadji da sauran membobin gwamnati da jami´an diplomasiya da shugaban hukumomin yankin da kuma kungiyoyin ba da agaji. Guteres ya ce wata tawagar wakilan gwamnati da na hukumar sa da na hukumar samar da abinci ta MDD sun kai ziyarar farko a yankunan da aka ware don sake tsugunar da ´yan gudun hijirar. A gobe Guteres zai kai ziyara gabashin kasar ta Chadi inda dakarun gwamnati ke fafatawa da na ´yan tawaye.