1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar kiwan lahi ta Majalisar Dinkin Dunia ta kalubalanci masu sarrafa magani a bayan fage

February 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7m

A wani zaman taro da ke gudanarwa a birnin Rome na kasar Italia,Hukumar kiwon lahia ta Majalisar Dunia Dunia, ta bukaci a kara matsa kaimi, wajen yaki da masu sarrapa maganin assibti na bayan fage.

WHO, kokuma OMS, ta dangata wannan aiki, da kashin kai, ta la`akari da yadda, masu sarrafa maganin ba su da wata cikkakar kurewa, ta fannin kiwon lahia.

Jami´in hukumar lahia ta dunia, mai kulla ta kimiyar kirkiro magani, Howard Zucker, ya bayyana cewar, hukumar, za ta nemi tallafin jami´an tsaron kasa da kasa, wato Interpol, domin taimakawa wajen wannan yaki.

Wani mai magana da yawun kungiyoyin masu saida magani a Pharmacie, kokuma Kyamus, ya shawarwarci tanadar dokoki masu tsanani, ga dukan wanda aka samu, su na sarrafa magani ko su na saida shi a bayan fage.

Ya bada misali da wasu yara a kasar Haiti, da su ka rasa rayuka a sanadiyar shan wani maganin tari, da ya hito daga kasar China, wanda kuma su ka saya, wajen yan saida magani na kan titina.

Kazalika a kasar Kenya, wasu karin mutanen, sun kwanta dama, a dalili da anfani da magani na bayan fage.