1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukumar kare hakkin jamaa ta mdd ta fara zama a yau

Zainab A Mohammed.June 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu6Z

A yau ne sabuwar hukumar kare hakkin biladama ta mdd ta kaddamar da zamanta na farko a birnin geneva,tare da fatan cewa zata tallafawa wadanda ake takewa hakkokinsu ,ba tare da da laakari da banbancin siyasa kamar yadda aka fuskanta a tsohuwar hukumar da aka rusa ba.a jawabinsa na kaddamar da wannan zaman na mako biyu wanda ya kunshi wakilan kasashe 47,sakatare general na mdd Kofi Annan yace,duniya ta sanya idanu musamman kann mutanenda ke cikin hali na kunci saboda hakkokinsu da suka rasa.Sabuwar majalisar ta maye gurbin hukumar kare hakkin jamaa ta mdd wanda aka rusa saka makon zargin rashin adalci domin mafi yawan wakilan kasashen nada tarihin take hakkin jamaa.Akan hakane Annan ya bukaci sabbin wakilan dasu bawa mara da kunya wajen sauke nauyi daya rataya a wuyansu.

Jim kadam bayan kaddamarwar ,shugabar kungiyar kare hakkin jama ta human right watch ,Mariette Grange,ta tofa albarkacin bakinta a dangane da wannan sabuwar hukuma……………….

Sabuwar hukumar kare hakkin jama ta mdd zata cigaba da zaman taron nata na tsawon makonni biyi,akarkashin jagortancin Luis Alfonso de alba na kasar Mexico.