hukumar kare hakkin jamaa ta Majalisar dinkin duniya tayi Allah wadai da Israila | Labarai | DW | 06.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

hukumar kare hakkin jamaa ta Majalisar dinkin duniya tayi Allah wadai da Israila

Hukumar kula da kare hakkin bil adama ta MDD ta kada kuriar Akkh wadai da matakin soji da Israila ta dauka akan zirin Gaza.

Haka kuma tace zata aike da tawagar masu bincike ta MDD zuwa zirin Gaza,wadanda zasu duba batun take hakkin bil adama da akeyi a yankin.

Wannan jefa kuria kuwa tazo ne a bayanda jiragen yakin Israila suka ci gaba da luguden wuta dare na tara a jere a zirin Gaza.

A birnin Beit Lahiya dake arewacin Gaza,an kashe mutum guda a karo na farko gaba da gaba tsakanin dakarun Israila da Palasdinwa tun shigar Israilan Zirin Gaza.

Dakarun na Israila kuma sun sake mamaye wasu tsoffin matsuganan yahudawa yan share wuri zauna da suka janye tunda farko.