Hukumar Kare haƙƙoƙin jama´a ta UN ta matsa lamba ga Sudan | Labarai | DW | 30.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Kare haƙƙoƙin jama´a ta UN ta matsa lamba ga Sudan

Hukumar kare haƙƙoƙin jama´a, ta Majalisar Ɗinkin Dunia, ta ƙara matsa lamba, ga hukumomin Sudan, a game da halin da ake ciki a yankin Darfur.

A cikin yarjejniyar da membonin hukumar su ka rattabawa hannu, sun nuna matukar damuwa, a kan uƙuba da masifa, da gwamnati ke ganawa al´umommin wannan yanki.

Yarjejeniyar, ta buƙaci kafa wani komiti na mussamman, wanda kakakin haɗin gwiwar ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bil adama na ƙasar Sudan Sima Samar, zai jagoranta, tare da taimakon ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin jama´a, na AU, da na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Wannan komiti na da yaunin ci gaba da lalubo hanyoyin samar da zaman lahia, da kuma bin diddigin aiwatar da ƙa´dojin da Majalisar Ɗinkin Dunia ta tanada a game da wannan rikici.

Komitin zai gabatar da rahoton sa na farko, a watan juni mai zuwa.