Hukumar IAEA zata ci-gaba da tattaunawa a Vienna | Labarai | DW | 04.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar IAEA zata ci-gaba da tattaunawa a Vienna

Majalisar gwamnonin hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA zata kara matsawa Iran lamba har sai ta canza alkibla a takaddamar da ake yi dangane da shirinta na nukiliya. A ci-gaba da taron ta a birnin Vienna, a yau ne ake sa ran cewa hukumar zata amince da daftarin kudurin da KTT ta gabatar mata. Kudurin ya yi kira da mika wannan rikici na shirin nukiliyar Iran a gaban kwamitin sulhun MDD. Amma gwamnati a birnin Teheran ta ce muddin aka yi haka to zata fara aikin samar da sinadaran uranium gadan-gadan. Kudurin zai ba Iran wa´adin zuwa watan maris na ta ba hukumar IAEA cikakken hadin kai ko kuma a dauki matakai akanta ciki har da kakaba mata takunkumai.