Hukumar IAEA ta tabbatar da rufe tashar nukiliya ta Koriya ta arewa | Labarai | DW | 18.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar IAEA ta tabbatar da rufe tashar nukiliya ta Koriya ta arewa

Shugaban hukumar kula da kare yaduwar nukiliya ta kasa da kasa Muhammad El Baradei yace supetocin Majalisar dinkin duniya sun tabbatar da cewa Koriya ta arewa ta rufe dukkanin injunanta na nukiliya 5 dake tashar nukiliya ta Yongyon.

El baradei ya fadawa manema labari a birnin Kuala Lumpur cewa suna sa ran nan da yan makonni masu zuwa zasu ci gaba da daukar mataki da suka dace na sa ido ga rufe tashar ta nukiliya.

Yace hakan dai wani babban mataki ne mai muhimmanci amma kuma kuma da sauran aiki a gaba na game da batun makamn nukiliya na Koriyan.