Hukumar gudanarwa ta babban bankin duniya ta janye kanata daga laifin shugabanta | Labarai | DW | 13.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar gudanarwa ta babban bankin duniya ta janye kanata daga laifin shugabanta

Hukumar gudanarwa ta babban bankin duniya ta janye kanta daga laifin da shugaban bankin ya aikata na karin albashi ga wata maaikaciyar bankin tana mai baiyana cewa shugaban bankin Paul Wofowitz shi kadai ne ya kamata ya dauki wannan laifi na yiwa budurwarsa karin albashi.

Membobin hukumar gudanarwar sun kuma baiyana cewa zasu gaggauta daukar mataki akan shugaban bankin.

Wajen wani taron manema labari dai a ranar alahamis Wolf, ya amincewa cewa yayi kuskure ya kuma nemi gafara game da karawa matar Shaha Riza matsayi.

Wannan rikici dai yana kokarin yin barazana na mamaye taron karshen mako na babban bankin da kuma hukumar bada lamuni ta duniya a birnin washington.