Hukumar FAO ta bukaci samar da taimakon abinci ga kasar Sudan | Labarai | DW | 18.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar FAO ta bukaci samar da taimakon abinci ga kasar Sudan

Hukumar Majalisar Dinkin Dunia, mai kulla da bada tallafin abinci wato FAO, ta yi kira ga kasashen dunia da su gagauta kai agajin abinci a kasar Sudan, inda mutane a kalla million 7 ke fuskantar barazanar, fadawa cikin matsananciyar yinwa.

Hukumar na bukatar tattara dalla million 40, domin sayen abinci da irin shibka ga manoman kasar.

Tunnin Kungiyar PAM, ta ware ton dubu 731, da za ta fara rabawa a kwanaki masu zuwa.

A wani labarin kuma, shugaba Bush na Amurika, a karo na farko na bayyana amincewa da tura dakarun kwantar da tarzoma, na kasa da kasa, a yankin Darfur, na kasar Sudan, da ke fama da yake yake.

Wannan rundunar bisa jagorancin Majalisar Dinkin Dunia, zata kunshi kimanin dakaru dubu 14, wanda za su karu ga sojojin kungiyar tarayya Afrika su dubu 7.

Kungiyyar tsaro ta NATO a shire ta ke, inji Bush ta bada mahimiyar gudummuwa ga wannan runduna.