Hukumar EFCC ta Najeriya ta fara binciken wasu ’yan majalisar ƙasar saboda tuhumarsu da ake yi na karɓar cin hanci da rashawa. | Labarai | DW | 15.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar EFCC ta Najeriya ta fara binciken wasu ’yan majalisar ƙasar saboda tuhumarsu da ake yi na karɓar cin hanci da rashawa.

Hukumar nan ta EFCC, mai binciken batutuwan cin hanci da rashawa da almubazarrabnci a tarayyar Najeriya, ta ce ta fara gudanad da bincike a kan wasu ’yan majalisar ƙasar, waɗanda ake zargi da karɓar cin hanci don amincewa da yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar kwaskwarima da burin share wa shugaba Olusegun Obasanjo fagen aiwatad da shirinsa na zarcewa da mulki a wa’adi na uku.

Wata sanarwar da hukumar ta bayar yau a birnin Abuja, ta ce tuni, jami’anta sun fara bin diddigin zargin da ake yi wa ’yan majalisar, tare da ziyarar wasu bankuna da ofisoshi a babban birnin na tarayya. A halin yannzu dai, hukumar na kira ne ga duk jama’an ƙasar da ke da hujjoji kan wannan zargin, da su fito su bayyana musu su, don hakan zai sauƙaƙa wa jami’anta aikinsu.

’Yan majalisar ƙasar masu adawa da shirin ta zarcen, na zargin wasu takwarorinsu ne da karɓar cin hanci na kimanin Naira miliyan 50 daga gwamnati don su goyi bayan shirin yi wa kundin tsarin mulkin kwaskwarima.

Tun 1999 ne dai shugaba Obasanjo ya hau karagar mulki a zaɓen dimukraɗiyya da aka gudanar a ƙasar. A shekara ta 2003 ne kuma, ya ci gaba da mulkin bayan sakamakon zaɓen da aka gudanar ya tabbatar masa da rinjayi. Sai dai, a halin yanzu goshin ƙarshen wa’adinsa bisa yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanadar, wasu muƙarrabansa na yunƙurin cim ma yi wa kundin kwaskwarima don ya iya zarcewa da mulki a wa’adi na uku.