1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hukumar Ciyad da Duniya da Abinci ta yi gargaɗin barkewar bala’in yunwa a Korea Ta Arewa.

A yayin da ake ta bukukuwan ƙaddamad da ranar abinci ta duniya yau a yankuna daban-daban na duniya, Hukumar Ciyad da Duuniya da Abinci, ko kuma WFP a taƙaice, ta yi gargaɗin cewa, idan ba a samo ƙarin taimakon abinci daga ƙetare ba, to ƙasar Korea Ta Arewa za ta huskanci wani bala’in yunwa a lokacin sanyi na wannan shekarar. Ƙarancin taimakon abinci da ake samu daga ƙetare ya kara taɓarɓare al’aumra a ƙasar, inji Michale Huggins, kakakin hukumar ta WFP:-

„Muna cikin wani matsanancin yanayi ne a halin yanzu. Hukumar Ciyad da Duniya da Abinci dai na iyakacin ƙoƙarinta. Amma mutane miliyan ɗaya kawai ne tallafinmu ke kai gare su. Yayin da ake shiga cikin lokacin sanyi kuma, kashi 10 cikin ɗari na kuɗaɗen da muke bukata ne kawai muke da shi a halin yanzu. Bisa dukkan alamu dai, za a shiga cikin wani mawuyacin hali ne a lokacin sanyin.“