Hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya za ta ƙara kai agaji ga ƙasashen sahel
April 21, 2010Hukumar cimakka ta majalisar dinkin duniya FAO ta bada sanarwa ƙara ƙarfafa agajin da ta ke bayarwa manoma da makiyaya a ƙasashen Nijar da Cadi wanɗanda ke fuskantar ƙarancin abinci a sakamakon fari da ake fama da shi a ƙasashen sahel.Hukumar ta yi gargaɗin cewa rashin kyaukyawar daminar da ba a samu ba a shekara bara ba na iya yin barazana ga kimanin mutun miliyion 9,8 a cikin ƙasashen wanda wasu ke cikin halin yunwa a arewacin Burkina Faso da arewa maso gabacin Mali, dakuma Nijar.Ƙungiyar ta FAO ta ce ta ƙaddamar da tsare tsare domin kawo talafi ga al uma a cikin ƙasahen,misali a ƙasar Nijar ta ƙaddamar da projet na dala Amurka miliyion 12 da al uma miliyion biyu da rabi zasu ci moriyarsa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Abdullahi Tanko Bala