1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hukuma na kokarin shawo kan rikicin Mambila

June 22, 2017

  A yayin da ake ci-gaba da zaman dardar a karamar hukumar Sardauna dake cikin jihar Taraba, gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce ta tura karin soja don magance lamarin

https://p.dw.com/p/2fD8Z
Protest Ölpreis Nigeria Januar 2012
Hoto: Reuters

 

Tun a cikin tsakiyar makon jiya ne dai wani rikicin fili a tsakanin kabilun Mambila da Fulani ya rikide zuwa babban rikicin da ya kai ga asarar rayuka na Fulani kusan dari dama raunata shanu kusan 17,000.

Wani taro na manema labarai a banagaren wata kungiyar kare muradi na fulanin yankin na tsaunin Mambila dai, ta bukaci kaddamar da dokar tabaci a daukacin jihar ta  Taraba, bayan abin da ta kira kau da kai na gwamnatin jihar wajen kyale kisan na Fulani.

 Kungiyar kare fulanin wace aka sani da Pastoral Resolve, ta bakin sakatarenta da ke riko Dakta Sale Momale, ta zargi hukumomin yankin da hana bada agaji ga fulanin da rikicin ya rutsa da su, tare kuma da toshe kafofin isar da taimako a cikin yankin. Ko da yake gwamnatin jihar ta Taraba tuni ta yi watsi da wannan tuhumar da ake yi mata.