Hugo Chavez na ziyara Algeria da Lybia
May 16, 2006Talla
Shugaban ƙasar Venezuela Hugo Chavez, ya fara ziyara aiki a nahiyar Afrika.
A matakin farko na wannan ziyara, ya yada zango a ƙasar Algeria, a sahiyar yau talata.
Wannan shine na karo na 3, da shugaba Hugo Chavez, ya ziyarci Algeria.
A shekara ta 2000, da kuma 2001, ya ziyarci wannan ƙasa, a matsayin ta na member, a ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun man petur.
Chavez, da Abdoul-Aziz Buteflika, sun yi masanyar ra´ayoyi ,a game da harakokin diplomatia na dunia, da kuma saye da sayarawa.
A jajibirin wannan ganawa, tawagogin ƙurraru na ƙasashen 2,, su yi mahaurori, jiya litinin , a game da harakokin makamashi, noma,da ilimi, da kuma zirga zirga.
Bayan Algeria shugaban ƙasar Venezuela zai ziyarci Lybia.