HRW ta zargi gwamnatin Sudan da aikata kissan kiyasu a yankin Darfur | Labarai | DW | 07.09.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

HRW ta zargi gwamnatin Sudan da aikata kissan kiyasu a yankin Darfur

Hukumar kare haƙƙoƙin bani adama, Human Rigth Watch, ta zargi hukumomin Sudan, da aikata kissan kiyasu ga al´ummomin yankin Darfur.

Kakakin hukumar, Peter Takirambude, ya ce binciken da su ka gudanar ya gano hanyoyin da dakarun gwamnati ke bi, domin hallaka al´ummomin da ba su ji, ba su gani ba, tare da anfani da bama bamai.

Sudan ta bayyana aniyar jibge, dakaru dubu 10 a wannan yanki, domin maye gurbin sojojin shiga tsakani na ƙungiyar taraya Afrika.

A wata sanarwa da ta hido jiya laraba, fadar gwamnatin Amurika, ta bukaci sojojin AU, su ci gaba da zama, a yankin, kamin ya´Allah Sudan, ta amince karɓar rundunar shiga tsakani ta MDD.