Hotunan video da aka nuna akan Abdulmutallab | Labarai | DW | 27.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hotunan video da aka nuna akan Abdulmutallab

An baiyana wasu hotunan video da ke nuna ɗan Nageria nan da ya kai harin da ya ci tura a cikin watan disamber da ya gabata ya na samun horon Alƙaida

default

 Wasu hotunan video da ƙungiyar Alƙaida ta baiwa ƙasar Yemen, sun nuna Umar Farouk Abdulmutallab ɗan Nageriya nan wanda ya yi yunƙurin kai wani harin ta jirgin sama a Detroit da ya ci tura a lokacin  sallah krismety da ta gabata ya na samu horo daga yan ƙungiyar alƙaida.

Videon dai ta nuno Farouk din da wasu sauran jama'ar na alƙaida a sai'ilin da ya ke baiyana sarnawa cewa a shirye ya ke ya mutu a  cikin jahadi na yaƙar yahudawa,  da krista.

A cikin watan janeru da ya gabata matashin dan shekaru 23, ya ƙi ya amsa laifufuka har guda shidda, waɗanda suka hada da aikin  ta'adanci dakuma neman aikata kisa gila  akan fassinjoji 290 da wata Kotu a Detroit ta zargeshi da aikatawa,kuma idan har aka sameshi da laifi to kam za' iya fuskantar hukumci ɗaurin rai da rai.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        :  Zeinab Mohamed Abubakar