1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Horst Köhler: Kimar Turai ta zube a idanun Afirka

Abdullahi Tanko Bala
February 20, 2017

Tsohon shugaban Jamus Horst Köhler ya ce sakamakon kura-kurai na siyasa da aka yi, Turai na rasa kimarta a idanun Afirka ya na mai cewa Afirka na kara samun kwarin gwiwa da karfin zuciyar taimakon kai da kai.

https://p.dw.com/p/2XuWt
Berlin 15th International Economic Forum on Africa
Hoto: cc-by-nc-Frederic Schweizer

A wata makala da ya gabatar a birnin Berlin, tsohon shugaban kasar ta Jamus Horst Köhler ya ce wajibi ne kasashen yamma su saurari nahiyar Afirka da kunnen basira, ya na mai cewa ta haka ne kawai za a samar da tsari da manufa mai nagarta da za ta dace da bukatun da ake da su a kasa. Sai dai kuma a halin yanzu sabanin haka ne ke wakana a cewar Köhler inda ya ke cewa babu wani kudiri na wanzar da ci-gaba mai dorewa a Afirka, a maimakon haka ya ce sai matakai aka dauka na rage yawan 'yan Afirka da ke shiga nahiyar Turan. 

Entwicklungsminister stellt in Kenia Aufbauplan für Afrika vor
Jamus na kokari wajen habaka dangantaka ta tattalin arziki tsakaninta da AfirkaHoto: picture alliance/dpa/B. Otieno

Da ya ke tsokaci kan kalmar nan ta habaka ci-gaba na Marshall Plan da ministan raya kasashe na Jamus Gerd Müller ya bayyana aiwatar wa domin Afirka, tsohon shugaban na Jamus ya ce ''ina jin cewa manufar ta raya kasa wadda ta hada da zamantakewar al'umma an yi ta da niyya ta alheri, amma kuma akwai fargaba kada a bata rawa da tsalle bisa ga tsarin ita kanta manufar ta raya kasa.” Köhler dai na goyon bayan shawarwari da dama da ke kunshe a jadawalin shawarwarin na habakar ci-gaban kasa na Marshall Plan, alal misali habaka kawancen kasuwanci wanda zai taimaka wajen samar da miliyoyin ayyukan yi ga 'yan Afirka.

Wani abu har wa yau da ya tabo shi ne kawance tsakanin kamfanoni masu zaman kansu da kasashen Afirka, koda yake wasu manazarta na ganin cewa kamfanoni masu zaman kansu na daukar Afirka a matsayin wata kasuwa mai armashi, yayin da wakilan wasu kungiyoyin farar hula ke zargin wasu kamfanonin na kasashen waje ciki har da Jamus da ci da gumin 'yan Afirka ta hanyar karbe musu filaye da gonaki ko kuma biyan ma'aikata a nahiyar da ke yi musu aikin kwadago kan dan abin da bai taka kara ya karya ba.