Horst Köhler ya yi murabus. | Labarai | DW | 31.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Horst Köhler ya yi murabus.

Murabus na shugaban Jamus bisa sukan da ya sha a baya-bayan nan.

default

Hoerst Kohler, yayin ba da sanarwar murabus ɗinsa.

Shugaban ƙasar Jamus, Horst Köhler ya ba da sanarwar yin murabus ba da ɓata wani lokaci ba. A wani taron manema labrai na gaggawa da ya shirya, shugaban na Jamus ya ce ya tsai da wannan shawara ne sakamakon sukan da ya sha game da wasu kalamai da yayi a baya-bayan nan akan aikin da dakarun Jamus ke yi a ƙetare. Bayan wata ziyara da ya kai wa dakarun Jamus da ke aiki a Afganistan, Koehler ya nunar da cewa tura dakarun Jamus zuwa ƙetare dai mataki ne da a wasu lokuta ya biya buƙatun tattalin arzƙin ƙasar. 'Yan adawa sun kira waɗannan kalamai tamkar abin da ya saɓa wa ƙudurin Jamus na ƙin tura dakarun zuwa ƙetare, da ta naƙalta bayan yaƙin duniya na biyu. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta dakatar da ziyarar da ta yi shirin kai wa ƙungiyar ƙwallon ƙafar Jamus domin tunkarar wannan ci gaba. Kamar dai yadda kundin tsarin mulkin Jamus ya tanada, Jen Boehrsen, magajin garin Bremen da ke zaman shugaban babbar majalisar dokokin shi ne zai karɓi ragamar shugabancin.

Mawallafiya: Halimatu Abbas

Edita: Yahouza Sadissou Madobi