Horas da limaman musulmi a Turai | Zamantakewa | DW | 14.01.2009
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Horas da limaman musulmi a Turai

Limamai a nan Jamus na da babban tasiri akan musulmai mazauna wannan ƙasa ta hanyar Fatawar da suke bayarwa

default

Ministan cikin gidan Jamus Wolfgang Schaeuble da kakakin majalisar ƙungiyoyin musulmi a Jamus Bekir Alboga

Suna ba da shawarwari na shari´a wato Fatawa wanda ta haka suke taka rawa a rayuwar yau da kullum ta al´umar musulmin wannan ƙasa.

Tun shekaru masu yawa da suka wuce ake muhawwara a nan Jamus akan horas da limamai. Akwai dubban limaman na addinin Musulunci a masallatai dake a tarayyar ta Jamus to amma kimanin kashi 90 cikin 100 sun fito ne daga ƙasar Turkiya sai wasu ɗaiɗaiku daga ƙasashen Marokko da kuma Iran. Waɗannan limaman ba su iya Jamusanci ba saboda haka ba su da masaniya game da al´amuran siyasa, zamantakewa da kuma al´adun wannan ƙasa. Waɗannan limaman suna da tasiri a rayuwar musulmai a wannan ƙasa musamman game da Fatwa da suke bayarwa. Ferid Heider limami ne a wasu masallatai biyu dake birnin Berlin yayi bayani game da muhimmancin Fatwar ga rayuwar musulmi.

“Kowane musulmi na da damar yanke shawara dangane da wanda zai zama masa jagora. Alal misali ba dole ba ne in yi aiki da Fatawar da ta fito daga jami´ar Azhar ta ƙasar Masar ko wadda ta fito daga wasu masana addinin musulunci. A matsayina na musulmi, nauyin dake kai na shi ne in yi aiki da ilimi da kuma basirar da Allah Ya ba ni.”

Ferid Heider wanda ya girma a Berlin, a cikin gamaiyarsa ana yawaita yi masa tambayoyi game da abubuwan da suke halan ko haramun ga musulmi. Rayuwar yau da kullum a nan Jamus tana da sarƙaƙƙiyar gaske. Alal misali sau da yawa lokutan Sallah da na aiki ba sa dacewa da juna, ga zuwa koyan ninƙaya a makarantu ga yara mata sannan shan barasa ya zama ruwan dare a gidajen sayar da abinci. Limamin kan juya ga Alƙur´ani mai girma da Haddisan Annabi Mohammad SAW kafin ya ba da amsoshin tambayoyin da ake masa. Amsoshin da yake bayarwa suna dacewa da salon rayuwar yau da kullum a nan Jamus. Ya ce kamata yayi kowace Fatawa ta dace da ainihin abin da ake magana kai.

“Muna buƙatar malamai masana waɗanda ko dai a nan Turai suka tashi ko kuma sun daɗe a nan, waɗanda kuma suke da cikakkiyar masaniya game da halin siyasa, zamantakewa, tattalin arziki da dai sauransu a nan Turai. Ta haka za su iya ba da Fatawa ko shawarwari masu gamsarwa. Ina jin wannan shi ne ɗaya daga cikin ƙalubaloli masu muhimmanci dake gabanmu a nan Turai.”

A wasu ɓangarorin Fatawa daga nan Jamus ta bambamta da wadda ake bayarwa daga ƙasashen da musulmai ke da rinjaye. Hakan na da nasaba da yadda Fatwar ta ke domin an tsara ta ne yadda za ta dace da ainihin abin da ake batu kai. To amma duk da haka aikinta kan wuce ainihin abin da ake magana kai inji Bettina Gräf masaniyar kimiyar addinin musulunci ta cibiyar nazarin sabbin al´adun ƙasashen Larabawa dake Berlin.

“Akwai karin maganar nan da ke cewa duk abin da ba haramun ba ne to a fakaice halan ne. Saboda haka ake ƙoƙarin yin amfani da wannan karin magana don samun biyan buƙata. Tun a cikin shekarun 1990 Fatawa ta ɗauki sabon matsayi mai muhimmancin gaske wajen bayyana al´adu da ɗabi´un musulmai a Turai da kuma Amirka.”

Ɗaukacin manyan malaman shari´ar musulunci a ƙasashen da bisa al´ada na musulmi ne na nuna damuwa game da sabbin dokokin shari´ar Musulunci a Turai. Waɗannan malaman na fargabar cewa ´yan´uwansu musulmi a ƙasashen yamma ka iya kaucewa daga hanya madaidaiciya wanda a ƙarshe zai kai su daga barin addinin na musulunci. Don hana hakan aukuwa sun fid da wata Fatawa kan yadda suke ganin dacewar rayuwa a Turai. Farfesan shari´a Matthias Rohe masani ne na shari´ar musulunci ya nuna damuwa game da wannan Fatawa daga ƙasashen musulmi.

“Yawancin Malamai a waɗannan yankuna, su da kansu ne ke tsara tambayoyin da suke son su ba da amsoshinsu. Ba sa bari a yi musu tambayoyi. A gani na wannan wani ci-gaba ne mai tattare da ayar tambaya a cikinsa. Ana samun Fatawa musamman ma daga ƙasar Saudiya kan yadda musulmi za su tafiyar da rayuwarsu a nan Turai wato kamar yadda za su nesanta kansu da sauran jama´a, zaɓan irin abincinsu da rashin cuɗanya da sauran al´uma waɗanda ba musulmi ba. Abin takaici shi ne hukuma ce ke tallafawa wannan farfaganda ta ƙoƙarin yaɗa aƙidar wahabiyawa a nahiyar Turai. Wannan wani ci-gaba ne mai haɗarin gaske.”

Musulunci dai addini ne da bai da wani shugaba takamaime wato saɓanin a majami´ar Katholika inda ake da Fafaroma dake zama shugaban dukkan mabiya majami´ar ta Katholika. Saboda haka ake samun saɓanin ra´ayi tsakanin tsakanin limaman addinin musulunci inda kowane ke ƙoƙarin samun magoya baya da yawa. Masu matsanancin ra´ayin addinin da masu sassaucin ra´ayi da ke goyon bayan kyakkyawan zaman cuɗe-ni in cuɗe-ka, kowanensu na ganin yana da ta sa hujja a cikin Fatawa. Hatta su ƙungiyoyin addinin musulunci a nan Jamus na ƙoƙarin jawo hankalin musulumi da su san irin nauyin da addinin ya ɗora musu, domin saɓanin ra´ayi na addini na kawo ciƙas ga aniyar musulmin ta gabatar da wata tsayayyar ƙungiya da za ta wakilce su baki ɗaya inji Burhan Kesici sakatare janar na majalisar musulmi ta tarayyar Jamus.

“Ina ganin buƙatarmu a nan Jamus da ma a Turai baki ɗaya shi ne yadda za a ba da muhimmanci ga wakilan musulmai a tattaunawar da ake yi. Amma ba kawai a ci-gaba da nuna cewa ai rashin samun wani tsayayyen shugaba ya sa kowane musulmi gaban kansa ya ke, saboda haka ba za mu iya magana da yawun dukkan musulmi ba. Hakan zai sa a shiga wani sabon yanayi inda musulmin za su ɗauki makomar su a hannunsu ko kuma su nemi wata hanyar da don su samu biyan buƙata.”

Wannan hanyar kuwa ita ce za ta share fagen shiga tattaunawa da cibiyoyin gwamnati musamman idan ana magana game da tsara manhajar koyar da darussan musulunci a makarantu ko shawarwarin fasalta wasu dokoki. Ko shakka babu ƙungiya za ta iya yin tasiri ga matsayin imanin ɗaiɗaikun mutane, inji Burhan Kaseci inda ya ƙara da cewa ana iya mayar da membobi masu matsanancin ra´ayi ko masu wata niya ta daban saniyar ware.

Sauti da bidiyo akan labarin

 • Kwanan wata 14.01.2009
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/GYSz
 • Kwanan wata 14.01.2009
 • Mawallafi Mohammad Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/GYSz