Hollande: Boko Haram na ci gaba da zama barazana | Labarai | DW | 14.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hollande: Boko Haram na ci gaba da zama barazana

Shugabannin kasashen Yankin Yammaci na Afirka da na kewayen tafkin Chadi da kuma sauran kasashen duniya na duba hanyoyin yaki da Boko Haram a taron da suka soma a birnin Abuja na Tarrayar Najeriya.

Nigeria Boko Haram Krisengipfel Francois Hollande und Muhammadu Buhari

Shugaba Hollande da shugaba Buhari a taron tsaro na Abuja

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya bayyana a ranar Asabar din nan cewa har yanzu Kungiyar Boko Haram na ci gaba da zama barazana ga kasashen da ke kewayen tafkin Cadi duk kuwa da irin nasarar da ake samu ta murkushe kungiyar.

Shugaba Hollande ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga taron manema labarai a Abuja fadar gwamnatin Najeriya bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari gabannin bude taron koli na yaki da ta'addanci wanda Najeriyar ke karbar bakuncinsa a karo na biyu.

"Kungiyar 'yan ta'addar da ta yi kaurin suna wajen kisan ba gaira, da kisan fararen hula da yin garkuwa da yara mata, misali yara 'yan makarantar Chibok, an kora 'yan ta'addar sun gudu, sun bar wurare da suka kama a lokutan baya, sai dai har yanzu 'yan ta'addar na ci gaba da zama barazana."

Yayin wannan taron koli dai ana sa ran ya maida hankali kan kaddamar dakarun hadin gwiwar kasashen na Najeriya da jamhuriyar Benin da Kamaru da Cadi da Nijar su yi aiki tare da karasa murkushe mayakan na Boko Haram a yankinsu.