Holland ya lashe amansa kan yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima | Labarai | DW | 30.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Holland ya lashe amansa kan yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima

Shugaban Faransa ya yi watsi da shirinsa na janye fasfunan Faransawa da aka samu da laifin aikata ta'addanci.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya janye shirinsa da ake takaddama kai, na yi wa kundin tsarin mulkin kasa kwaskwarima, da zai ba da damar janye fasfunan Faransawa da aka samu da aikata tarzoma. Hollande ya ce ya gano cewa ba a samu daidaito ba tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai game da shawarar ta sa. Bayan hare-haren ta'addancin da aka kai a birnin Paris a watan Nuwamban shekarar 2015, shugaba Hollande ya ba da sanarwar yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska da ya tanadi janye 'yancin zama dan kasa ga duk Bafaransen da aka samu da laifin ta'addanci. Tuni dai ministar shari'ar kasar Christine Taubira ta yi murabus sakamakon takaddamar da ta kunno kai saboda wannan yunkuri.