1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Holland ta dauki dokar hana sanya nukabi

Gazali Abdou Tasawa
November 29, 2016

Majalisar dokokin kasar Holland ta kada kuri'ar amincewa da dokar haramta saka nikabi da burqa a wuraren taruwar jama'a a fadin kasar. Duk matar da take keta dokar zata biya tarar Euro 405.

https://p.dw.com/p/2TSpq
Niederlande Amsterdam Frauen mit Vollverschleierung
Hoto: picture-alliance/ANP/R. Vos

Majalisar dokokin kasar Holland ta kada a wannan Talata kuri'ar amincewa da dokar haramta saka nikabi da burqa a wasu wuraren taruwar jama'a kamar makarantun boko da gidajen asibiti da jiragen kasa da motocin safa. Da kuri'u 132 daga cikin 150 dokar ta samu amincewar majalisar.

A nan gaba ne majalisar dattawan kasar za ta saka hannu kan wata dokar ta daban da ta tanadi hukunci na tarar kudi da ka iya kai har Euro 405 ga duk mutuman da za a samu da aikata laifin karya matakin. 

Hukumomin kasar ta Holland sun bayyana cewa dokar na da burin ganin an iya tantance duk wani mutun da zai shigo mutane wannan kuwa a bisa dalilai na tsaro. Tuni dama kasashen Beljiyam da Bulgeriya da wasu yankunan kasar Switzerland suka soma amfani da wannan doka ta haramta saka nikabi.