1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Holland: Hukunci kan safarar makamai

April 22, 2017

Wata kotun kasar Holland ta sami wani tsoho dan shekara 74 da laifin sayar wa tsohon shugaban kasar Liberia Charles Taylor da makamai.

https://p.dw.com/p/2bk3Q
Fall Srebrenica Urteil gegen Holland Flash-Galerie
Hoto: picture alliance/dpa

Kotun wadda ta yanke masa daurin shekaru 19 na dauri, ta ce ta gano mutumin da ke dillancin katako, ya yi wasu kamfanoni biyu a kasar Liberia a farkon shekarun 2000, ya kuma yi amfani da kamfanonin nasa wajen safarar makamai zuwa kasar ta Liberia. Kotun dai ta yanke masa hukunci ne saboda laifin taimaka wa yaki, da kuma ke zama laifi irin na yakin.