Hizboullah ta bukaci gwamnatin Libanon yin murabus | Labarai | DW | 23.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hizboullah ta bukaci gwamnatin Libanon yin murabus

Rahotanni daga Libanon na nuni da cewa wasu dubbannin masu zanga zanga sun daddatse manyan titunan birnin Beirut.

Hakan kuwa yazo ne a dai dai lokacin da kungiyyar Hizboullah ta kira wani yajin aikin sai baba ta gani, da ake shirin farawa yau.

Masu zanga zangar dai na bukatar gwamnati mai ci a kasar ne karkashin Firaminista Fouad Sinora yin murabus.

Tuni dai kafafen yada labarai suka rawaito faraministan na cewa jami´an tsaro zasu yi duk iya bakin kokarin su, wajen tarwatsa masu zanga zangar don samar da hanya ga yan kasar dake son zuwa guraren aikin su.

Kungiyyar dai ta Hizboullah a cewar rahotanni na adawa ne da gwamnatin ta Mr Sinora, bisa zargin da suke cewa yar koren kasashen yamma ce.