Hissein Habre zai ci gaba da zama kasar Tchad har zuwa taron kungiyar AU | Labarai | DW | 28.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hissein Habre zai ci gaba da zama kasar Tchad har zuwa taron kungiyar AU

Ministan harakokin wajen kasar Senegal, ya baiwa tsofan shugaban Tchad Hissein Habre, damar ci gaba da zama Senegal , har zuwa taron koli, na kungiyyar taraya Afrika, da za a yi a watan janairu mai zuwa a kasar Sudan.

Wannan sanarwa ta biwo bayan wadda ministan cikin gidan Senegal, yayi ranar assabar da ta wuce,inda ya bayyana mika Hissein Habre a hannun kungiyar AU, bayan da kotunan kasar sun kasa yanke hukuncin dassa keyar sa, zuwa kotun Belgium.

Gwamnatin Senegal,ta yanke wannan shawara bayan tantanawar da a ka yi ,tsakanin Shugaba Abdulay Wade ,da Oleshegun Obasanjo, shugaban kungiyar Tarraya Afrika.

A yammacin jiya, jami´an tsaro, sun shiga gidan Hissein Habre inda su ka yi rijistan dukan dukoyoyin da ya mallaka.

A cen kasar Fransa gungun masu goyan bayan sa da su ka kaffa kungiya, sun yi Allah wadai da wannan abu, da su ka kira tozarta tsofan shugaban , sun kuba zargi gwamnatin kasar Senegal, da taka dokokin kasa da kasa a game da batun gudun hijira.