Hisbollah ta yi watsi da shawarar dakatar da yaki
July 21, 2006Kungiyar Hisbollah ta bi sahun Isra´ila wajen yin watsi da kiran da babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi na a tsagaita bude wutar yakin da ake yi tsakanin Isra´ila da Hisbollah. Wakilin Hisbollah a majaliasar dokokin Libanon Hussein Hajj Hasan ya fadawa kamfanin dillancin labarun AFP a yau juma´a cewa abin da zasu amince da shi shi ne wani shirin tsagaita wuta ba tare da gindaya sharadi ba da tattauna batun yin musayar firsinoni. Shi ma shugaban Hisbollah a Libanon Sheikh Hassan Nasrallah ya yi watsi da sakin sojojin Isra´ila da ake garkuwa da su ba tare da an yi musayar su da firsinonin Falasdinawa dake gidajen kurkukun Isra´ila ba. A jiya dai ne Mista Annan ya ba da shawarar a sako sojojin Isra´ila biyu da Hisbolah ta yi garkuwa da su kana kuma a dakatar da yakin nan take.