1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hisbollah ta shirya gudanar da zanga-zanga a Beirut

Kungiyar Hisbollah da sauran kungiyoyin ´yan adawa a Libanon sun yi kira da a gudanar da wata zanga-zangar gama gari da za´a fara gobe juma´a a birnin Beirut da nufin kifar da gwamnatin FM Fuad Siniora mai adawa da Syria. An yi kiran ne a cikin wata sanarwar hadin guiwa da aka karanta ta gidajenn telebijin na Hisbollah da sauran ´yan adawa. Jim kadan bayan wannan sanarwa shugaban Hisbollah Hassan Nasrallah ya bayyana a tashar telebijin ta Almanar ya na mai cewa gwamnatin FM Siniora ta gaza saboda haka ya kamata a kafa wata sahihiyar gwamnatin hadin kan kasa. Za´a gudanar da babban taron gangami ne a tsakiyar birnin na Beirut inda ofisohin FM Siniora suke.