Hisbollah ta lalata wani jirgin ruwan yakin Isra´ila | Labarai | DW | 15.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hisbollah ta lalata wani jirgin ruwan yakin Isra´ila

Sojojin Isra´ila 4 sun bata bayan an lalata wani jirgin ruwan yakin Isra´ila a wani hari da dakarun kungiyar Hisbolah suka kai kan sa a kusa da gabar tekun Lebanon. An yi imanin cewar an kai harin ne da wani jirgin sama da ake sarrafa shi daga nesa wanda aka cika masa makamai. Kamar yadda rundunar sojin Isra´ila ta nunar, harin ya kuma kuskure ya afkawa wani jirgin ruwan Masar. Da farko shugaban Hisbollah Hassan Nasrallah ya fadawa tashar telebijin ta Hisbollah cewa a shirye suke su gwabza yaki da Isra´ila. Hakan kuwa ya biyo bayan harin da jiragen saman yakin Isra´ila suka kai ne akan hedkwatar Hisbollah dake kudancin Libanon da kuma kan gidan shugaban kungiyar a Beirut. Hakazalika jiragen saman yakin Isra´ila sun kuma harba rokoki akan birnin Sur mai tashar jiragen ruwa dake kudancin Libanon. ´Yan sanda sun ce kiris ya rage rokar ta afkawa wani asibiti dake kusa. Amma ´yan sanda sun ce mutane 4 ciki har da wani Bamasare daya sun rasu sannan 12 sun jikata a hare haren da Isra´ila ta kai yau a Libanon.