Hiroshima: Koriya ta Arewa ta soki Amirka | Labarai | DW | 27.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Hiroshima: Koriya ta Arewa ta soki Amirka

Koriya ta Arewa ta cacccaki Shugaba Barack Obama kan ziyararsa ta birnin Hiroshima na Japan wanda Amirka din ta jefawa makamin nukiliya karshen yakin duniya na biyu.

Japan G7-Gipfel Barack Obama Pressekonferenz in Ise-Shima

Obama shi ne shugaban Amirka ta farko da ya ziyarci Hiroshima tun bayan yakin duniya na biyu

A wani sharhi da kamfanin dillancin labaran Koriya ta Arewan na KCNA ya fidda a jiya Alhamis, ya ce shawarar da Obama ya yanke ta ziyartar Hiroshima daidai ta ke da wasan yara, inda a hannu guda ya soki Japan kan amincewar da ta yi Obama din ya ziyarci birnin.

Ziyarar ta Obama dai ita ce irinta ta farko da wani shugaban Amirka ya taba kaiwa birnin na Hiroshima tun bayan da jirgin yakin Amirka ya jefa makamin nukiliya a birnin a cikin shekarar 1945. Yayin wannan ziyara dai, ana sa ran shugaban na Amirka zai ajiye furanni don tunawa da kuma girmama kimanin mutane dubu 140 wanda suka rasu lokacin da aka jefa bam din.