Hira da shugabar haɗin gwiwar ƙungiyoyin fara hulla a Tchad | Siyasa | DW | 18.04.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hira da shugabar haɗin gwiwar ƙungiyoyin fara hulla a Tchad

Shugabar haɗin gwiwar ƙungiyoyin fara hulla a ƙasar Tchad Delphine Kemneloum Djiraibe ta yi hurici a game da rikicin tawayen Tchad.

default

Ƙungiyoyi masu zaman kansu, a Tchad sun yi huruci, a game da tashe -tashen hankullan da ke ci gaba da gunada, a wannan ƙasa.

Kakakin Haɗin gwiwar ƙungiyoyin sa ido, da bin diddiƙin wanzuwar zaman lahia, Mai sharia´a Delphine Kemneloun Djiraibe ,ta bayyana abubuwan da sanarwar da ƙungiyar su ta hido su ka kunsa:

Sanarwar ta ƙunshi rukuni 3,

na farko, mun gayyaci ɓangarori daban- daban, masu yaƙar juna da su ajje makamai, su koma tebrin shawarwari, domin warware rikicin da ya haɗa su, cikin ruwan sanhi.

Sannan, mun buƙaci shugaba Idriss Deby, ya fassa shirya zaɓen shugaban ƙasa na ranar 3 ga watan mai kamawa, wanda a dalilin sa ne, rikicin Tchad ya ƙara ƙamari.

Sannan a mataki na 3, mun yi kira ga ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa, da ƙasashe masu hannu da shuni, da su taimaka wa Tchad, amma taimako na zahiri, domin ta hita daga halin da ta tsinci kanta a ciki.

Wato,su daina ɗaurewa shugaba Idriss Deby gidi, a alwashin da ya sha, na sai ya shirya zaɓen shugaban ƙasa a ranar 3 ga watan Mai.

Ƙasar Tchad ta shiga wani hali, inda ta hanyar zaɓe ko kuma ta hanyar ɗaukar mulki da tsinin bingida, ba zai sa a samu bakin warware rikicin ƙasar ba.

A game da haka, doli wannan shawawari da mu ka bada wato aje makamai da fasa zaɓe sune kaɗai za su iya shawo kann rikicin.

Mun tabatar da cewa akwai, matsaloli masu tarin yawa a ƙasar Tchad, wanda su ka sa wasu daga al´ummomin wannan ƙasa su ka shiga tawaye ,domin kwatar yancin su, da ƙarfin tuwa.

Abinda kuma, mu ke bukata shine, al´ummar Tchad baki ɗaya,, su zuba ma zukatan su ruwa, su zauna tebrin shawarwari domin daidaita kansu,ba wai kawai ,a yi ta zargin wata ƙasa ba, da cewar itace ke rura rikicin a Tchad.

Lalle mu na cikin damuwa, domin bamu da tabbas a game da abubuwan da kann iya faruwa a cikin mintina ko sa´o´i masu zuwa.

Akwai tawagogin soja da ke ci gaba da sintiri cikin birnin N Djamena.

Sannan yan siyasa na ɓangaren gwamnati da na yan tawaye na ci gaba da hiddo sanarwoyi ta kaffofin sadarwa, da su ka saba wa juna, a kan haka a gaskiya mu an cikin ruɗani.

Mu na ƙara kira ga shugaba Idriss Deby, a kan yaunin da ya rataya a wuyan sa, na magance wannan matsala.

A nasa ɓangare yau ne shugaban Tchadin yayi kiran taron manema labarai, inda ya ƙara jaddada cewar babu shaka Sudan ce, ke hasada rikicin tawaye a Tchad.

 • Kwanan wata 18.04.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0Y
 • Kwanan wata 18.04.2006
 • Mawallafi Yahouza Sadissou
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu0Y