Hira da ministar raya kasa ta Jamus | Siyasa | DW | 08.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Hira da ministar raya kasa ta Jamus

A hira da aka yi da ita ministar raya kasa ta Jamus ta bayyana muhimmancin demokradiyya ga zaman lafiyar Kongo

A lokacin ziyarar, ministar taimakon raya kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul ta sadu da shugaban kasar Kongo Joseph Kabila da sauran jami’an gwamnatinsa da kuma wakilan ‘yan hamayya, wadanda suka mika godiyarsu ga Jamus dangane da gudummawar da kasar ta bayar tare da takwarorinta na Kungiyar Tarayyar Turai lokacin zaben demokradiyya na farko da aka gudanar a Kongo shekarar da ta wuce. A mayar da martani ga wannan godiyar Heidemarie Wieczorek-Zeul cewa tayi:

“Dukkan matakan da muka dauka da kuma wadanda muke dauka a halin yanzu na da nufin bayyanarwa da al’umar kasar ne cewar ba kawai goyan baya muka ba wa zaben da aka gudanar ba, kazalika muna sha’awar ganin an samu ci gaba a fafutukar tabbatar da zaman lafiyar kasar da kuma tabbatar da ita akan tsarin mulki na demokradiyya.”

Heidemarie Wieczorek-Zeul ta kara da cewar a shawarwarin da ta gudanar tare da jami’an gwamnati da wakilan ‘yan hamayya ta bayyanar musu a fili cewar ba kamata a samu wata tangarda a hadin kai tsakanin gwamnati da ‘yan hamayyar ba ta la’akari da irin nauyin da ya rataya wuyansu baki daya. A sakamakon haka ta gudanar da shawarwari tare da wakilai masu yawa na ‘yan hamayya. Muhimmin abin dake akwai shi ne girmama tsarin dokokin kasa da tabbatar da mulkin demokradiyya da girmama hakkin dan-Adam.

Dangane da albarkatun kasa da Allah Ya fuwace wa Kongo, wanda kuma ake wawasa ba ji ba gani, to kowace irin gudummawa Jamus zata iya bayarwa domin tinkarar wannan matsala..Heidemari Wieczorek-Zeul ta ka da baki ne ta ce:

“Da farko dai zamu ba da gudummawa wajen ganin matakan da aka gabatar sun zama masu tasiri. A halin yanzu haka akwai kasashe masu tarin yawa da suka hada da na Afurka da Nahiyar Turai dake taka muhimmiyar rawa a wannan kyakkyawan ci gaba, kuma Jamus na fatan gabatar da maganar a zauren taron kasashen G8 da za a gudanar a kasar don neman goyan baya a fafutukar kawo karshen fasakwabrin albarkatun kasar ta Kongo da ake yi ba ji ba gani. Wannan mataki yana da muhimmanci saboda shi ne zai taimaka wajen dakatar da wannan ummal’aba’isi wanda ta kansa ne kungiyoyin ta da zaune tsaye ke samun kudaden shiga don ci gaba da ta’asarsu a maimakon amfani da su wajen yakar talauci. Kazalika wannan mataki zai taimaka wajen tinkarar matsalar cin hanci.”